Tsakure
Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni daban-daban cikin salo mabambanta. Wannan ya sanya waƙa ta zama sha-kundum, har ake yi mata kallon magani ga dukkanin abin da ake da cutarsa. A wannan maƙala, an yi ƙoƙarin bibiyar wasu waƙoƙin situdiyo domin a fito da misalan turakun da suke ƙunshe cikin waƙoƙin baka na situdiyo, wanda hakan ya nuna cewa lalle waƙoƙin baka na situdiyo sun zama magani ga kowace irin damuwa a cikin al’umma. Wannan nazari ya yi ƙwai da ƙyanƙyasa a farfajiyar waƙoƙin na situdiyo, inda aka taɓo turke kaɗai domin fito da A’i daga rogo, sannan aka yi ƙoƙarin bayyana wasu waƙoƙi a kowane ɓangaren da suka shafi rukunin da aka ajiye su. Yayin gudanar da binciken, an bi hanyoyi da dama da kuma yin amfani da dabaru, inda aka yi ƙoƙarin nemo waƙoƙin da kuma sauraronsu sauraronsu, da zaƙulo irin abin da ake buƙata a waƙar, domin ishara zuwa ga gaɓar da ake magana a kai. A wannan bincike, an yi ƙoƙarin ɗora shi a kan Ra’in Mazahabar Nason Adabi a Aladu (Folk-Cultural Theory) wanda Williams Bossom ya ƙirƙire ta, sannan aka sami mabiya daga ƙasar Amurka waɗanda suka bi ta. Wannan bincike ya ƙarƙare da zayyano sakamakon da aka samu yayin gudanar da shi.
Fitilun Kalmomi: Zamfara, Kafafen Sada Zumunta, Tashe-Tashen Hankula
Authors: Ibrahim Baba et al.