Tsakure
Matsalar tsaro a jihar Zamfara ta shafi kowa da kowa. Gwamnatoci da hukumomi da ɗaiɗaikun, Mutane, kuma a cewar kowanne yana bayar da gudummawa wajen daƙile wannan matsalar. Daga ɓangaren makaɗan baka tuni ba tun yau ba, a cikin waƙoƙinsu suke nusar da jama’a wasu abubuwan da idan da an yi riƙo da su da ba a samu kai a halin da ake ciki yanzu ba. Abubuwan ne wannan takarda, ta duba don ganin irin gudummawar da suka bayar ko jama’a ta yi tsinkaye ta koma kan ɗabi’unta da al’adunta na zamantakewa kyawawa. Makaɗan da aka kafa hujja daga waƙoƙinsu na yankin ƙasar Zamfara ne. Bahaushe kuwa yace; “Mai ɗaki shi yasan inda yake yi masa yoyo”.
Fitilun Kalmomi: Gudummawa, Makaɗan Baka, Tsaro, Zamfara
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.017
Authors: Kurawa, H.M. and Gummi, M.F.