Tsakure
Manufar wannan bincike ita ce zaƙulowa tare da faɗaɗa nazari a kan salon tsattsafi a cikin waƙa. Binciken ya mayar da hankali kan salon tsattsafin haliya. An ɗora nazarin bisa ra’ayin Yahya na “Salon Tsattsafi.” An keɓance nazarin kan zaɓaɓɓun waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) guda bakwai (7) waɗanda suke mazaunin samfurin binciken. An ɗauki waɗannan waƙoƙi a matsayin tushen bayani na farko. Tushen bayani na biyu da binciken ya yi aiki da shi, shi ne rubuce-rubucen masana da suka gabaci wannan. Binciken ya tabbatar da cewa, lallai mawaƙi na tsattsafin haliya ko haliyoyi a cikin waƙa. Haka kuma, yana iya tsattsafin haliya guda a cikin waƙoƙi daban-daban da ya shirya yayin da yake cikin yanayi iri guda. A bisa haka, binciken na ganin za a iya amfani da wannan salon nazari a matsayin matakin bincike kan halaye da ɗabi’u.
Fitilun Kalmomin: Tsattsafi, Haliya, Waƙa, Salo