Kishi A Bakin Makaɗan Baka

     Tsakure: Manufar wannan maƙala ita ce bitar ma’anar kishi da yanaye-yanayensa, musamman a tunanin Bahaushe. Maƙalar ta bi matakin nazartar waƙoƙin makaɗan baka a matsayin hanyar gudanar da bincike. A cikin waƙoƙin ne ta zaƙule yanaye-yanayen kishi a farfajiyar tunanin Bahaushe. An ɗora akalar nazarin kan tunanin Bahaushe cewa “So so ne, amma son kai ya fi.” A bisa wannan ra’ayin Bahaushe ne takardar ke da hasashen cewa, kowane mutum na da zummar samun ɗaukaka da fice sama da dukkannin tsaransa. Sakamakon binciken ya nuna cewa, ba kamar yadda mutanen da dama ke tunani ba, al’amarin kishi bai taƙaita ga abin da ake samu tsakanin masoya ba kawai. Ya shafi dukkannin ɓangarorin rayuwa. Sannan dalilai da dama na sa a bayyana kishi. Daga ƙarshe takardar ta ba da shawarar bin matakan da za su tabbatar da giyar kishi ba ta kai ga janyo aikata abin da ya saɓa wa hankali da kyakkyawar al’ada da zamantakewar lumana ba.

    Fitilun Kalmomi: Kishi; Waƙa; Makaɗa; Bahaushe; Hausa

    Yumsuk-Hausa E-Library

    Pages