Ƙabilu a Tunanin Bahaushe: Duba Cikin Labaran Barkwanci

    Cite this article: Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2022). Ƙabilu a Tunanin Bahaushe: Duba Cikin Labaran Barkwanci. In Sarcouncil Journal of Humanities and Cultural Studies 1.1, pp 27-32. ISSN (Online): 2945-3658 DOI:  https://zenodo.org/record/6418660. 

    Tsakure

    Manufar wannan maƙala ita ce nazartar nau’ukan labaran da ke yawo a bakunan Hausawa game da ƙabilun da ke hulɗayya tare da su. An zaɓi biyar daga cikin ƙabilun a matsayin samfurin wannan bincike. An bi manyan hanyoyi biyu domin tattara bayanan binciken. Na farko shi ne tattarawa da taƙaita tarihin haɗuwar Hausawa da ƙabilun da aka zaɓa cikin samfurin binciken. Na biyu kuwa shi ne nazarin fitattun labarai game da waɗannan ƙabilu. An ɗora aikin a kan tunanin Bahaushe na “da wayo ake faɗa wa wawa gaskiya.” Binciken ya gano cewa, bayan kasancewar waɗannan labarai abinci ga adabi, suna kuma da amfani ta fuskar faɗakarwa da nishaɗantarwa. A bisa haka ne takardar ta ba da shawarar samar da kwas na musamman game da barkwanci tare da inganta shi domin cin gajiyar hikimomi da damarmaki da ke tattare da wannan ɓangare na adabi tare da kauce wa ƙalubalen da ke ƙunshe cikinsa.

    Fitilun Kalmomi: Barkwanci, Labarai, Fulani, Buzaye, Nupawa, Yarbawa, Inyamurai

    Yumsuk-Hausa E-Library

    Pages