Dusashewar Wasannin Gargajiya A Ƙasar Yabo

    Wannan bincike ya ƙudiri aniyar yin bayani ne a kan dusashewar wasu wasanin gargajiya na yara a ƙasar Yabo. “Dusashewar wasu wasanin gargajiya na yara a ƙasar Yabo”, wanan zai ba, mai karatu damar sanin ire-iren wasannin gargajiya, da yadda ake aiwatar da su, da kuma lokacin aiwatar da su, da kuma tasirin zamani a kansu, sannan da sanadiyyar dursashewarsu.

    Haka kuma wannan zai ba yara matasa sanin yadda waɗannan wasanni ke gudana, tare da sanin sunayen wasannin. Masana da dama sun yi bayani a kan ma’anar wasa. Wannan aikin ya yi tsokaci a kan wasu daga ma’anonin da suka ba wasa.

    An tsara wannan aiki, babi-babi har zuwa babi biyar, domin samun sauƙin karantawa ga mai nazari. Har-ila-yau aikin ya yi nazarin waɗansu littattafai, da kuma wasu ayukkan da suka gabata domin ƙarin samun haske dangane da wannan aiki.

    Dalilin yin wannan bincike shi ne, domin duba ko binciko wani ɓangare na irin wannan tsarin wasannin.Wannan zai ba da damar ganin irin dusashewar da wasannin gargajiya ke samu. Saboda ganin muhimmancin wasanni, aikin binciken nan ya ƙudiri aniyar ɗaukar ƙaramar hukumar domin yin bayanin wasannin na Hausawa da suka gudanar tun daga ƙuruciyarsu har zuwa tasowarsu. Wanda kuwa, wasannin su ne ke ƙulla zumunta har zuwa tsufa.

    Ganin irin wannan muhimmancin da ke tattare da wasanni ya kyautu a gudanarda aikin bincike a kansu. Wannan aiki na sa ran ya kasance mai amfani ga ƙananan makarantu (primary) har zuwa manyan makarantu (secondary). Ba su kaɗai ba ma, har da manyan yara na garin Yabo da kewaye. Amin.

    Yumsuk-Hausa E-Library

    Pages