Dangantakar Harshen Hausa Da A Nufanci: Nazarin Tasirin Hausa A Kan Harshen Nufanci

    Masana da manazarta daban-daban sun tofa albarkacin bakinsu a kan harshen Hausa da kuma harshen Nufanci, harsunan guda biyun su ne duk wanda yake É—an asalin harshen yake alfahari da shi kuma suna daga cikin harsunan nahiyar Afirka musamman Afirka ta yamma.

    Akwai amincewar masana ilimin kimiyyar harshe irin su Yakasai da Jinju a kan cewa, harshen Hausa yana cikin wani gundarin babbar rukuni na sauran harsunan duniya. Haka zalika, harshen Nufanci, ya keÉ“anta da É—imbin tarihi a idon duniya wanda wannan fage ba zai damar zuwa da su ba sai dai É—an kaÉ—an wanda a haÆ™iÆ™anin gaske, wasu dalilai ne suka haifar da rashin ci gaban harshen. Bugu da Æ™ari, akwai dangantaka da ke tsakanin harsunan nan guda biyu musamman ma dangantaka ta hulÉ—a da na kasuwanci da fatauci da auratayya da na aron kalmomi wanda a sanadiyar waÉ—annan dangantaka, ya kawo tasirin Hausa a kan Nufanci da dai makamantansu.

    Bayan haka, na karkasa wannan aiki zuwa babuka guda biyar domin samun damar bayyanar da kai da kuma samun nasarar kammalawar aikin. A babi na farko, wato gabatarwa an yi bayanin abubuwa inda aka fara da shimfiÉ—a da manufar bincike da farfajiyarsa da muhimmancinsa da dalilansa da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar ci gaba da bincike da kuma naÉ—ewa. A babi na biyu, an yi bayanin tarihin hulÉ—ar al’ummun inda aka kawo taÆ™aitaccen tarihin

    Hausawa da na Nufawa da hulÉ—arsu da mazaunin Nufawa da kuma naÉ—ewa. A babi na uku kuwa, an yi bayanin dangantakarsu a fuskoki daban-daban da suka haÉ—a da ma’anar dangantaka da dangantaka ta addini da fatauci da zuwan Turawa da wasu kayan Æ™walamar Hausawa da É—inki da noma da kamun kifi da sabulun salo da daddawa da Æ™ira da kuma dangantakar auratayya sannan naÉ—ewa.

    A babi na huÉ—u kuma, an yi bayanin tasirin harsunan nan guda biyu a kan juna inda aka gabatar da shimfiÉ—a da ma’anar tasiri da yanayi da tsarin tasirin aron kalma da dabarun aiwatar da aron kalma da kashe-kashen aro da dalilan aro da matsalolin aro da kuma tasirin ararrun kalmomin Hausa daga Nufanci sannan naÉ—ewa. A babi na biyar kuma, an fara gabatar da shimfiÉ—a da sakamakon bincike da kammalawa da kuma shawarwari sannan kuma naÉ—ewa.

    Yumsuk-Hausa E-Library

    Author: Kudu Muhammad Salihu

    Pages