Al’adun Hausawa sun samu sauye-sauye da dama a goshin ƙarni na ashirin da ɗaya. Bisa ga haka, za a ga cewa wasu al’adun suna salwanta wasu kuma suna gurvata, kai ka ce ba ma na Hausawa ne ba. Kamar irin su al’adun aure da na haihuwa da na zamantakewa, da dai sauran makamantansu. Wannan shi ya Ƙarfafa mini guiwar yin wannan bincike a kanrawar mata ke takawa wajen sauya fasalin bukukuwa a garin tsafe.
Author: Sadiya Yakubu