Dalilin da ke sa a gudanar da bincike suna ɗauke da manufofi daban-daban kamar yadda ake aiwatar da shi binciken. Saboda haka, dalilan da suka sa aka gudanar da wannan bincike suna da yawa, amma ga wasu kamar haka:
(a) Babban dalili na ɗaya ga aiwatar da wannan bincike shi ne, cike wani gurbi da masana suka manta da shi cikin littafan da suka rubuta, waɗanda ba su yi magana a kan su ba. A fannin al’ada Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, ya rubuta littafi a fannin al’adar, amma bai ambaci sana’ar gini da magini (Birkila) ba duk da sanin kowa ne al’umma ba za ta iya rayuwa babu muhalli ba.
(b) Dalili na biyu kuwa, shi ne, rashin tsayuwar masana su yi zuzzurfan bincike a kan sana’ar gini da magini (Birkila), sai dai a shafi wurin sama-sama a wuce, misali kamar: Farfesa, Ibrahim Yaro Yahaya da wasu (1992), sun kawo sana’o’in Hausawa na gargajiya, inda suka ambaci sana’ar gini a ciki, amma ba a yi bayanin sana’ar tiryan-tiryan ba, kamar yadda ya kamata. Madogarata ita ce littafin nasu mai suna “Darussan Hausa don manyan makarantun sakandare (1992). A nan ne suka kawo sana’o’in.
(c) Dalili na uku, fannin al’ada sashe ne da yake da fatara irin ta ƙarancin masana a gefen. Saboda ko a ɓangaren wasu al’adun za a ga cewa al’adun suna cikin hatsari (endangered) kamar gini da magini (Birkila).
Author: Hisbullahi Danlami