An daɗe ana gudanar da bincike a kan abin da ya shafi lamarin karuruwan harshen Hausa, tun daga rabe-rabensa har ya zuwa nazarin ɗaiɗaikun karuruwan harshen, kamar su: Sakkwatanci da Katsinanci da Zamfaranci da Kabanci da dai sauran kare-karen harshen Hausa. Da farko dai kafin a ce komai, ya kamata a san ƙunshiyar wannan babi da ke ƙoƙarin bayyana abubuwan da suka shafi nazarin da ake son gudanarwa. A wannan babi na farko yana da bayanan abubuwa da suka haɗa da, bitar ayyukan da suka gabata, da dalilin yin bincike, da hanyoyin gudanar da bincike, da kuma muhimmancin bincike. Don haka waɗannan abubuwa da aka ambata, su ne za a gabatarwa, a kaso na gaba in da za a fara da bitar ayyukan da suka gabata.
Author: Naziru Muhammad Alkali