Ko a cikin al’adun Hausawa ma, al’adar aure babbar al’ada ce. Tun kafin zuwan Musulunci Hausawa suna da irin al’adun da suke gudanarwa yayin bukukuwan aure. Al’adun sun haɗa da gayyata da kai lefe da sayen baki da kitso da lallai da makamantansu. Irin waɗannan al’adu na aure sun samu sauye-sauye lokacin da addinin Musulunci ya iso ga Hausawa. Al’adun aure da Musulunci ya zo da su sun haɗa da addu’an ɗaurin aure da neman izini kafin magana da budurwa da makamantansu. Da tafiya ta yi tafiya kuma, zamani ya sake kawo wasu al’adun na daban cikin lamurran auren Hausawa. Irin al’adun da zamani ya zo da su yawanci na Turawa ne da Indiyawa da Kuma Labawa. Sun haɗa da fati, da ranar uwa, da sauransu.